Babban Mashawarcin Shugaba Muhammadu Buhari a Harkokin Majalisar Dattawa, Ita Enang, ya bayyana cewa gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari na daga daga cikin gwamnatocin da suka fi aiki da gaskiya a kasar nan.
Enang ya yi wannan kalami ne yayin da Kungiyar Lauyoyin Jihar Akwa-Ibom ta kai masa ziyara a Abuja.
Daga nan sai ya yi kira ga lauyoyin da kuma daukacin ‘yan Nijeriya su rika tuntubar jami’an gwamnati kan su tsaye, a kan duk wani al’amari na gwamnati da ba su fahimta ba, ko kuma su ke neman karin bayani a kai.

Ya ce yin haka shi ne mafi muhimmanci, maimakon a rika tafiya a na yi wa gwamnati mummunar fahimta.
Dangane da zargin da wasu ke yi cewa gwamnati na kokarin dabaibaye majalisar tarayya, Enang ya ce wannan zargin ma ga duk wanda ya san abin da ya ke yi, to ba abin kamawa ba ne.
“Bai ma yiwuwa gwamnati ta dabaibaye majalisar tarayya. Abin da kawai gwamnati ke nanatawa shi ne majalisa ta rika gudanar da ayyukan ta a kan ka’idar da doka kasa ta shimfida.
“A baya-bayan nan ai mun ga hukuncin da kotuna suka yanke har sau hudu, inda kotunan suka ce Majalisa ba ta da ikon aiwatar da abin da ta ce za ta aiwatar din.”
“Misali, majalisa ta rika dora wa wani laifi har ta na kiran wai ya je a gaban ta ya yi bayani, ko ya kare kan sa, wannan ba aikin ta ba ne, doka ba ta ba ta wannan karfin ikon ba. To irin wannan ne gwamnati ke yi wa majalisa nuni da cewa ta daina shiga hurumin da ba na ta ba.” Inji Enang.