Dole ‘yan Najeriya su fara shirin yin sallama da shinkafar kasar waje tun yanzu domin kuwa gwamnati ta kammala shirin rufe iyakokin Najeriya da kasashen dake iyaka da ita don hana shigowa da shinkafar kasar waje da yan kasuwa ke yi.
Ministan Ayyukan Gona Audu Ogbe ne ya bayyana haka da yake amsar bakuntar kungiyar matasa na GOTNI a Abuja.
Ogbe ya ce kasashen da Najeriya ke makwabtaka da su na neman karya tattalin arzikin kasa Najeriya ta hanyar dakushe kokarin manomar kasar nan. ” Hakan ya zama dole mu rufe iyakokin kasar nan kwata-kwata kawai saboda manomar mu su maida hankali wajen noma shinkafa yadda ya kamata.”
” Babban matsalar mu shine fasakwarin shinkafa da ake yi zuwa kasar nan daga kasashen dake makwabtaka da mu. Sannan kuma shi wannan shinkafar kasar waje ma bata da inganci domin duk an riga an gurbatata. Idan kaci ma cuta ce kawai zaka ciwa kanka.
” Dole mu maida hankali wajen inganta noman shinkafa a gida, bawai mu tsaya wasu na yi mana abin da suka ga dama ba sannan manoman mu na wahala babu kasuwa. Za mu rufe boda kwata-kwata kowa yaci shinkafar gida.

” Ni ne manomi na farko da ya fara noman shinkafa sannan na sarrafa ta babu kasa ko daya a kasar nan.
Ogbe ya ce gwamnati za tayi haka domin ceto manoman kasar nan da ‘yan Najeriya da kuma tattalin arzikin kasar nan.
Discussion about this post