An fi cinikin maganin zubar da ciki a Najeriya da Ghana – Bincike

0

Gidan jaridar BBC ta gudanar da bincike inda ta gano cewa kasashen Najeriya da Ghana na cikin kasashen Afrikan dake yawan neman magungunan zubar da ciki a yanar gizo.

BBC ta bayyana cewa Najeriya da Ghana kasashe ne da suka kafa dokokin dake hukunta mace ko likitan da ya cire wa mace ciki idan ba dai cikin ya nuna alamun cutar da lafiyar mai dauke da shi bane.

Amma duk da wannan doka, mata da wasu likitocin da basu kware a aikin su ba kan cire wa mata ciki a boye.

Bayan haka jaridar ta bayyana cewa shigowar fasaha kamar su yaran gizo da wayewar kai ya sa mata na iya karya wannan dokar ba tare sun fuskanci hukuncin ba.

Bisa binciken da suka gudanar matan kasashen Najeriya da Ghana kan yi amfani da yanar gizo wurin siya da koyan yadda ake amfani da wani maganin cire ciki mai suna Misoprostol.

” Misoprostol magani ne dake da ingancin cire cikin da ya kai tsawon kwanaki 50 ba tare da mace ta sami wani matsala ba.”

A yanzu dai sanadiyyar gano wannan magani na cire ciki matan wadannan kasashe basu damu da zuwa ko neman wani likita ba.

Bayanai sun nuna cewa a shekara miliyan 1.25 ne ke zubar da ciki, da daga ciki 34,000 ba a yin su yadda ya kamata sannan kashi 13 bisa 100 a cikin su kan rasa ran su sanadiyyyar haka a Najeriya.

Share.

game da Author