Idan ba a manta jim kadan bayan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari sanar da sauya ranar dimokradiyya daga 29 ga watan Mayu zuwa 12 ga watan Yuni domin karrama ranar da aka soke zaben da ake zaton marigayi Abiola ya yi nasara a kai, sanata Dino Melaye ya kushe wannan kokari na gwamnatin Buhari a zaman majalisar dattawa na wannan rana.
Dino ya mike tsaye, yana ta haki da gwalo idanu, jijiyoyin wuyar sa sun fiffito, a zauren majalisa ranar yana ya sukar wannan karramawa da Buhari ya yi wa Abiola.
Ya ce sam bai dace ayi masa wannan karamci ba sannan lambar girmamawa ta GCFR da aka bashi ma ba ayi daidai ba.
Dino ya kara da cewa idan ma za ayi wa batun fashin tonon silili Abiola ma ba dan Najeriya bane yanzu tunda ya riga mu gidan gaskiya.
Jawabin Dino bai yi wa mutanen da dama dadi ba inda da kansa ya ce ana ta kiransa daga mazabar sa cewa yaya ko zai furta irin wadannan kalamai.
Dino ya fito karara a yau Lahadi inda ya ke cewa lallai ba haka ya ke nufi ba wai ba a fahimci kalaman sa bane.
Ya ce yana kan gaba wajen kira da a karrama marigayi Abiola sannan ya sha kira da a sauya ranar dimokradiyya zuwa ranar 12 ga watan Yuni.