Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyna cewa ya hana Kakakin Yada Labaran sa Femi Adesina maida martanin wasikar Obasnanjo, saboda Adesina din yaro ne, shekarun sa ba su kai na gwada kwanji ko kirji da Obasanjo ba.
Buhari ya yi wannan bayanin a lokacin da Kungiyar Goyon Bayan Buhari, wato Buhari Support Group ta kai masa ziyara a fadar sa, a ranar Juma’a da dare.
Buhari ya kara da cewa dalili na biyu kuma da ya ga bai dace ya maida wa Obasanjo martani ba, shi ne saboda shi da Obasanjon duk tsoffin sojoji ne.
Sai dai kuma ya ce amma Ministan Yada Labarai Lai Mohammed da ya ki bin umarnin sa ya maida masa raddi, ya yi kokari sosai wajen martanin da ya yi wa Obasanjo.
Ya ce ya lura Lai ya maida karfi ne wajen bayyana wa ‘yan Najeriya halin da kasar nan ke ciki kafin su karbi mulki, cikin 2015 ta hanyar cin gadon mummunan damejin da aka yi mata.
“Ku kuma na yi murna ganin yadda ku ka yi amfani da watan Ramadan ku ka baro garuruwan ku ku ka zo domin kawo min ziyara., domin ku yi min murnar dan kokarin da muka samu muka yi daga hawan mu mulki zuwa yau.”
“Wato na ki sakin jiki mu maida wa Obasanjo amsar wasikar da ya rubuto min. Ga dai Femi sai kakkarwar saurin maida masa amsa ya ke yi, amma sai na ga ai shi yaro ne, bai kamata ya sa baki ba.
“Na biyu kuma ni da Obasanjo duk tsoffin sojoji ne, daga gida daya muka fito kenan. To ban san yadda martanin zai shafi Femi ba. Amma yayin da Lai ya ce min shi fa sai ya maida martani, kuma na saurari dalilan sa, na ga ba yadda zan yi kawai.
Buhari ya ce Lai ce masa ya yi shi babu ruwan sa ma da Obasanjo, amma kawai zai tunatar wa ‘yan Najeriya irin barnar da aka yi cikin shekaru 16 na mulkin demokradiyya, da kuma irin gaganiyar da mulkin na Buhari din ke y i wajen sake saisaita akalar tattalin arzikin kasar nan.
Daga nan sai shugaban ya kara jaddada wa kungiyar cewa zai ci gaba da gudanar da ayyukan ci gaban kasa, raya karkara da kuma inganta tattalin arzikin kasar nan, domin kowa ya ci moriyar gwamnatin sa.
Da ya ke jawabi, shugaba kungiyar Buhari Suppport Group, Abba Ali, ya ce kungiyar sa na da ofisoshi a jihohi 36 na fadin kasar nan da kuma Abuja sannan a kowace karamar hukuma 774 babu wadda ba su bude ofis ba.
Discussion about this post