Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya gana da shugabannin hukumomi da na rundunonin tsaron kasar nan a fadar gwamnati dake Aso Rock.
Wannan shine karo na uku da shugaba Buhari ke ganawa da wadannan shugabannin tsaro na kasar nan a cikin mako guda.
Ko da yake babu wanda ya ce wa manema labarai komai bayan sun fito daga wannan taro, ministan tsaro Mansir Dan-Ali ya bayyana cewa taron na da nasaba da tsaron kasa ne.