Goguwar iskar ruwa ya rusa gidaje 1,536 a jihar Jigawa

0

Shugaban hukumar bada agajin gaggawa na jihar Jigawa (SEMA) Sani Yusuf ya bayyana cewa goguwar iskar ruwa da aka yi ya rusa gidaje 1,536 a kauyuka 12 dake kananan hukumomi biyar a jihar.

Kananan hukumomin sun hada da, Dutse, Guri, Gumel da Kiyawa.

Yusuf yace a karamar hukumar Babura iskar ya shafi mutane 58 sannan ta kuma rusa gidaje 84 a kauyukan Ajja da Dorawa.

A karamar hukumar Dutse kuwa ya shafi mutane 273 iskar ta shafa sannan da gidaje 1247 a kauyukan Warwade, Saya-Saya, Sabon Gari, Jidawa, Tumballe, Sabuwar Takur da Jigawar Habu.

Iskar ta shafi mutane 305 kuma ta rusa gidaje 543 a kauyukan Dayin sannan a kauyen Gumel mutane 101 iskar ta shafa da gidaje 208 a karamar hukumar Guri.

A karamar hukumar Kiyawa iska ta shafi mutane 108 sannan ta rusa gidaje 228 a kauyen Shuwarin.

Ya roki masu hannu da shuni da su kawo wa wadannan mutane agaji.

Share.

game da Author