Najeriya ta kara yawan kwanakin hutun da ake ba mata idan suka haihu

0

Gwamnatin Najeriya ta kara yawan kwanakin hutun da ma’aikata mata suke yi idan suka haihu daga watanni 3 zuwa watanni hudu.

Jaridar ‘Punch’ ta ruwaito cewa Ministan kwadago Chris Ngige ya bayyana haka ne ranar Talata a taron kungiyoyoyin kwadago na kasa da kasa da aka yi a kasar Switzerland.

Kafin wannan karin kwanaki da akayi macen dake dauke da juna biyu na da ‘yancin samun hutu na tsawon makomin 12 zuwa shida kafin ta haihu sannan da makonni shida bayan ta haihu.

Duk da haka gwamnati ta kara musu makonni hudu domin samin hutun da ya kamata bayan sun haihu.

Bayan haka Ngige ya yi kira ga duk fannonin daukan aiki da su guji kafa dokokin da ka iya hana mata aiki ko kuma hana su samun wannan hutun.

Bayanai sun nuna cewa ma’aikatar kwadago ta hana mazan da matan su suka haihu hutu sanadiyyar rashin amincewar majalisar wakilai.

Amma gwamnatin jihar Legas ta amince ta ba mazan da matan su suka haihu hutun kwanaki 10 domin kula da matan da ‘ya’yan da suka haifa.

Share.

game da Author