Za a bude tashoshin kekuna a Abuja – Minista Bello

0

A ranar Litinin makon nan ne ministan babban birnin tarayya Abuja Muhammed Bello ya bayyana cewa nan gaba kadan za a bude tashoshin kekuna a garin Abuja.

Bello ya yi wannan alkawari ne da ma’aikatan hukumar kare hadura na kasa da sauran mutane suka yi tattakiya zuwa ofishin sa a Abuja domin tunawa da ranar tuka keke wanda majalisar dinkin duniya ta kebe.

Ya ce bude tashoshin kekuna a Abuja zai taimaka wajen tunatar da mutane irin muhimmancin da keke ya ke dashi musamman a harkar sufuri.

” Bari a tuka keke a garin Abuja zai taimaka wajen rage lalata muhallin mu, rage kashe kudin shiga motar haya, rage yawan cinkoso a titunan mu da sauran su.”

Ya kuma kara da cewa za a kebe hanyoyi na musamman a titunan Abuja domin masu tuka keke.

Share.

game da Author