Bincike ya nuna cewa maganin cutar sankarar bargo ‘ Leukemia’ na iya maganin cwarkar da sankarar kwakwalwa.
Bao Shigang tare da sauran likitocin dake ma’aikatar gudanar da bincike na ‘Cleveland Clinic’s Lerner Research Institute’ suka gano haka.
Shigang ya bayyana cewa maganin ‘Ibrutinib’ (maganin cutar sankarar bargo) na da ingancin hana cutar yaduwa a jikin mutum.
” A binciken da muka yi mun yi amfani da maganin Ibrutinib a jikin wasu berayen da suka kamu da cutar sankarar kwakwalwa inda muka ga maganin ya hana cutar yaduwa a jikin su.”
a karshe Shigang ya ce nan ba da dadewa ba za su fara gwada ingancin wannan magani a jikin mutane.
Ya ce idan dai suka sami sakamako mai kyau daga wannan gwaji hakan zai ba likitoci damar iya ceto rayukan mutanen dake fama da wannan cuta maimakon amfani da maganin ‘Temozolomide’ da a ganin su bai kai ingancin maganin ‘Ibrutinib’ ba.
Discussion about this post