Kungiyar ma’aikatan jinya na jihar kwara sun janye yajin aiki saboda nada dayan su kwamishina

0

Shugaban kungiyar ma’aikatan jinya da ungozoma ta Najeriya (NANNM)Joseph Adekanye na jihar Kwara ya sanar da janye yajin aikin da kungiyar ta soma tun ranar 26 ga watan Afrilu.

Joseph ya sanar da haka ne ranar litinin a garin Ilori, hedikwatar jihar Kwara.

Adekanye yace kungiyar ta amince ta janye yajin aikin ne saboda kara wa wani dan kungiyar mai suna Rifun Kolo girma da gwamna yayi sannan da nada shi kwamishina kiwo lafiya na jihar.

” Yanzu dai mun janye yajin aikin da muka shiga amma mun ba gwamnati wa’adin watanni shida domin ta biya mana bukatun mu, sannan muna sa ran nada daya daga cikin mu zai sa komi ya zo mana da sauki.”

Share.

game da Author