An lalata haramtattun makamai 5,870 a Zamfara

0

Kwamitin Shugaban Kasa Kan Raba Al’umma da Kananan Makamai a Gusau, ya lalata makamai har guda 5,870 wanda Gwamnatin Jihar Zamfara ta karbe.

An fara gudanar da aikin lalata makaman ne da aka karbe daga hannun wadanda suka mallake su ba kan ka’ida ba.

Akasarin makaman an karbe su ne daga maharan da suka jaddada tuba, kuma suka mika makaman da kan su ga gwamnati a karkashin wani shiri da ke hannun mataimakin gwamnan jihar, Ibrahim Wakkala.

An lalata makaman ne a babban filin bajekolin jihar Zamfara da ke Gusau, karkashin sa-idon shugaban kwamitin, Emmanuel Imohe.

Cikin wadanda suka halarci taron akwai Gwamna Abdul’aziz Yari, Mataimakinn sa Wakkala da kuma wakilai daga Kungiyar Tarayyar Turai, ECOWAS da UNPD da jami’an tsaro da kuma sarakunan gargajiya.

Shugaban Kwamitin, Emmanuel Imohe, ya ce baya ga aikin karbar makaman da lalata su, gwamanati kuma za ta tabbatar da an sake raya yankunan da wannan kashe-kashe ya yi wa illa.

Share.

game da Author