Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa za ta hada karfi da karfe da guiwa da asusun kula da al’amurar yara kanana na majalisar dinkin duniya (UNICEF) domin samar da abinci wa wadanda ke fama da matsanacin yunwa a Najeria.
Ma’aikatar ta ce yin haka ya zama dole musamman ganin cewa bincike ya nuna yara kanana da suka kai miliyan 2.5 ne suka fi fama da yunwa a kasar.
” Binciken ya nuna cewa kashi 20 bisa 100 na wadannan yara za su iya mutuwa sanadiyyar yunwan da suke fama da shi idan har ba’ayi wani abu akai ba sannan mafi yawa daga cikin su yara ne daga yankin arewa maso gabashin Najeriya.
Ministan lafiya Isaac Adewole yace gwamnati ta tsara shiri na musamman kan yadda za a kubutar da yaran da suka fi fama da yunwa a jihohi 12 dake arewacin kasar nan.
Jihohin sun hada da Adamawa, Bauchi, Borno, Jigawa, Kano, Katsina, Kaduna, Sokoto, Yobe, Zamfara, Gombe da Kebbi.
A karshe jami’in UNICEF Mohammed Fall ya yi kira ga Najeriya da ta ware isassun kudade domin ciyar da yaran da mata dake fama da yunwa a kasar.