Za mu ci gaba da kamawa mu na gurfanar da barayin gwamnati, duk da ba a hukunta su – Osinbajo

0

Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya za ta ci gaba da kama wadanda ake zargi da sace dukiyar kasa ta na gurfanar da su, duk kuwa da wahala da tarnakin da ake samu wajen yanke musu hukuncin daurin shekaru a kurkuku.

Ya kuma kara da cewa a zaman yanzu masu cin hanci da rashawa ne ke yakar gwamnati gadan-gadan, domin su tabbatar da cewa an ture Shugaba Muhammdu Buhari a kan mulki.

Osinbajo ya yi wannan jawabi ne a garin Akure, a ranar Alhamis, a wajen kaddamar da tsarin Hukumar Kula da Kanana da Matsakaitan Masana’antu ta Kasa, a jihar Ondo.

“Duk da har yau ba a yanke wa kowa hukunci dauri ba, ba mu damu ba, hakan ba zai hana mu ci gaba da gurfanar da su ba. In ya so a ci gaba da tafaka shari’un a kotu, komai daren dadewa.

“Yanzu maciya hanci da rashawa ne ke yaki da gwamnati ka-in-da-na-in, saboda so su ke yi su dawo cikin gwamnati. Amma da iznin Allah sun bar gwamnati kenan, faufaufau.”

Mataimakin na Shugaban Kasa ya kara da cewa masu neman kawar da gwamnatin Muhammadu Buhari don su dawo gwamnati, suna yi ne domin su dawo su karasa kassara Najeriya dungurungun.

Share.

game da Author