An cika shekara daya cur kenan tun bayan da wasu jami’an gwamnatin Muhammadu Buhari suka sace dabino har tan 200 da Saudiyya ta bayar sadaka a lokacin azumi. Sai dai kuma har yau an kasa gano barayin balle a hukunta su.
Gwamnatin Saudiyya dai ta bayar da tallafin dabinon ne a cikin azumin Ramadan na shekarar 2017, da nufin a raba wa ‘yan gudun hijirar Boko Haram da ke zaune a sansanonin gudun hijira da kuma sallatai.
An bayar ne sadaka domin musulmi da suka kai azuri su samu abin abuda-baki, kasancewa shi ne sunnar abin da aka fi so a fara ci idan an kai azumi.
Bayan an kawo dabinon a Najeriya, an gano cewa ba a raba shi kamar yadda aka ce a yi ba. Maimakon haka, sai aka rika ganin sa a kasuwannin Abuja, jihar Barno har ma da Kano ana sayarwa.
Hakan ya kai ga gwamnatin Najeriya ta fitar da takardar ban-hakuri ga gwamnatin Saudiyya, kuma ta yi alkawarin kamowa da hukunta barayin dabinon.
Karamar Ministar Harkokin Waje, Khadija Abba Ibrahim ce ta bada hakurin a madadin gwamnatin Muhammadu Buhari.
Dabido tan dari 200 dai ya na daidai da kilogiram 200,000 na dabino, ko kuma a ce rigizar buhun dabino har duhu 4,000.
Da Premium TIMES ta yi bincike, ta gano cewa dabinon ya kai na adadin naira miliyan 20.
PREMIUM TIMES ta tuntubi Ma’aikatar Harkokin Najeriya domin jin inda magana ta kwana, amma ba ta ce komai ba dangane da batun dabinon.
Kakakin Yada Labaran Ma’aikatar mai suna Tope Elias-Fatile, bai dauki waya ba duk da yawan kiran da aka yi masa. Kuma bai maida amsar sakon tes da aka yi masa dangane da batun kin hukunta barayin dabinon ba.