Zidane ya bar Real Madrid

0

Mai horas da ‘yan wasan Real Madrid, Zinedine Zidane, ya aje aikin horaswas da ya ke yi wa kungiyar, kwanaki biyar bayan Real din ta lashe Kofin Zakarun Turai a karo na uku a jere karkashin horaswar sa.

Shi kadai ne ya taba cin kofin sau uku a jere, kuma banda shi da Carlo Ancelotti da Bob Paisely, babu wanda ya taba cin kofin sau uku.

Ya ci kofin cikin 2016, 2017 da 2018.

Zidane mai shekaru 45 a duniya, ya bayyana ajiye aikin sa ne a yau Alhamis a wani taron manema labarai na gaggawa da kungiyar ta kira.

Zidane ya ce ba shi ne zai koyar da kungiyar a kakar wasa mai zuwa ba.

A lokacin da ya ke jawabi a wurin taro da manema labaran, har da Shugaban Kungiyar, Florentino Perez.

A cikin shekara biyu da Zidane ya yi, ya buga wasa 146, ya ci 105, kuma ba a taba cire Real a wasan siri-daya-kwale a Kofin Zakarun Turai ba.

Ya ce ya dauki matakin aje aiki ne don kashin kan sa, ba sabani ko rigima ce hada shi da shugabannin kungiyar ba.

“Tun jiya da dare ma na kira shugaban Real, wato Perez na shaida masa cewa, ni fa zan yi gaba. Shawara da yanke don kai na.

“Real na bukatar canjin mai horaswa da kuma canjin takun wasa. Ba rikici ne ya sa zan tafi ba. Ina son kungiyar kuma shgabanta ya na so na matuka, domin shi ne ya kira ni ya ba ni aikin horaswar.

“Duk da nasarorin da na samu, ina ganin lokaci ya yi da zan yi gaba domin a samu canji a kungiyar. Na san hukuncin da na daukar wa kai na ba zai yi wa dama dadi a zukatan su ba. Amma a yi min uziri, kuma a yi hakuri.”

Zidane ya ci kofi har guda 9 a cikin shekara biyu da rabi, a karkashin Real Madrid.

Duniyar kwallon kafa ta gigita da jin wannan labara, yayin da kuma tambayoyi uku na ta yawo a zukatan mutane, an rasa mai bayar da amsa a halin yanzu?

Tambayoyin su ne: Mene ne takamaimen ajiye aikin Zidene? Ina zai koma? Wa zai canje she?

Share.

game da Author