Babbar Kotun Tarayya da ke Kaduna, ta tura tsohon gwamnan jihar, Ramalan Yero Kurkuku.
Tsohon Gwamnan da shi da wasu mutane uku ne aka tura kurkuku, bayan da Hukumar EFCC ta gurfanar da su a gaban mai shari’a.
Babban Mai Shari’a na kotun, Mohammed Shu’aibu, ya ce a ci gaba da tsare su a kurkuku, har zuwa ranar 6 Ga Yuni.
Sauran wadanda ake tuhuma tare da gwamnan sun hada da tsohon minista Nuhu Waya, tsohon sakataren gwamnatin jihar, Hamza Danmahawayi da kuma tsohon shugaban jam’iyyar PDP na jihar, Abubakar Haruna.
Dukkan su hudun ba su amsa laifin zargin wawurar kudi da EFCC ta ce sun yi ba.
Ana zargin su hudun da karbar sama da naira miliyan 700 a daidai lokacin da ruruguwar zaben 2015 ta gabato.
Discussion about this post