Barayin jarabawa sun yi kaka-gida a manyan mukaman Najeriya – Shugaban JAMB

0

Shugaban Shirya Jarabawar Shiga Jami’o’i ta Kasa (JAMB), Is’haq Oloyede, ya bayyana cewa Najeriya dankare ta ke da gaggan barayin jarabawa masu rike da manyan mukamai a mulkin kasar nan a bangarori da dama.

Ya ce masu dauke da satifiket na bogi sun yi yawa a cikin gwamnati.

Oloyede ya yi wannan jawabi ne a wurin taya gwamnan jihar Osun, Rauf Aregbesola murnar cika shekaru 61 da haihuwa, a jiya Lahadi.

Ya yi magana a akan ilmi mai inganci, kuma mai amfani, ya na mai cewa ilmi a kasar nan ya na fuskantar babban kalubale, saboda manyan masu mulki a kasar nan duk gaggan barayin jarabawa ne, ko kuma su na da hannu a harkallar satifiket na bogi.

Ya ci gaba da cewa bambanci tsakanin kudaden harajin da ya tara da wanda na bayan sa ya tara, sun nuna cewa washawa da cin hanci sun yi wa kasar nan katutu.

“Yadda Hukumar JAMB ke tara abin da bai wuce naira milyan 52 daga kudaden fam da suran hanyoyi ba, kafin mu hau shugabancin hukumar, ya nuna yadda kasar nan ta kasance a hannun ‘yan wuru-wuru.

“Amma mu sai ga shi bayan mun kammala shirya jarabawar JAMB ta 2017, mun tara kudaden shiga har naira bilyan 9. Kuma na maida wa gwamnatin tarayya naira bilyan 7.8. A wannan shekarar ma naira bilyan 9 na tara wa gwamnatin tarayya.”

Share.

game da Author