Gwamnatin Tarayya ta amince a kashe wani kason kudi har naira biliyan 199 domin gina ayyukan raya kasa.
Wadannan makudan kudade za a kashe su ne a karkashin Shirin Ingantawa da Raya kasa na Ofishin Shugaban Kasa.
Majalisar Shawarta Tattalin Arzikin Kasa ce ta fitar da wannan jawabin kafa wannan gidauniya domin samar da ababen more rayuwar yau da kullum ga ‘yan Najeriya, ranar Alhamis.
Shugaba Buhari ne ya amince da kafa gidauniyar inganta ayyukan raya kasar a taron majalisar zartaswa da ya gabata.
Za a fitar da wadannan zunzurutun kudaden ne daga ribar iskar gas da gwamnatin tarayya ke tarawa a cikin asusun ta na musamman da ke cike da wadannan makudan kudade a Babban Bankin Tarayya (CBN).
Ana kuma sa ran za a fi bada karfi ne wajen gina titina da kuma ayyukan da suka jibinci hasken lantarki a sassa daban-daban na kasar nan.
Wasu daga cikin ayyukan sun hada da titin, Kano-Kaduna-Abuja, tashar wutan lantarki na Mambila da sauran su.
Discussion about this post