Gwamnatin Amurka ta tallafa wa Najeriya da dala miliyan 90 da yayi daidai da naira biliyan 32 don yin kididdiga da sanin yawan masu dauke da Kanjamau
Ministan kiwon lafiya Isaac Adewole ya bayyana cewa gwamnatin kasar Amurka ta tallafa wa Najeriya da dala miliyan 90 don a san ainihin yawan mutanen dake dauke da cutar Kanjamau a kasar.
Ya fadi haka ne ranar Alhamis bayan sa hannu a takardar yarjejeniyyar da sukayi da wakilan gwamnatin a Abuja.
” Mun sa hannu a wannan yarjejeniyar tare da Jakadan kasar Amurka a Najeriya Stuart Symington da shugaban Hukumar Hana yaduwar cutar Kanjamu (NACA) Sani Aliyu.”
Adewole yace bayan Amurka ta bada wannan tallafin za kuma ta aiko da kwararrun ma’aikatan binciken da za su taya kasar gudanar da wannan bincike da za a fara daga watan Yunin 2018.
” Za ayi wannan bincike da kididdiga a dukka jihohin kasar nan sannan zai dauke mu watanni 6 muna yi. Wannan aiki zai taimaka wa gwamnatin Najeriya tsara manufofi da hanyoyin da zai taimaka wajen kawo karshen yaduwar wannan cuta.
Bayan haka Shugaban hukumar hana yaduwar cutar kanjamau (NACA) Sani Aliyu ya yaba wa wannan tallafi da Najeriya ta samu yana mai cewa hakan zai taimakawa kasar samar da wasu dabarun da zai kawo karshen yaduwar a kasar.
Discussion about this post