Oshiomhole ya fito takarar shugabancin APC

0

Tsohon gwamnan Jihar Edo, Adams Oshiomhole, ya fito ya bayyana aniyar sa ta takarar shugabancin jam’iyyar APC.

Tsohon gwamna wanda ya taba yin shugabancin kungiyar kwadago ta kasa, NLC, ya bayyana wannan aniya ta sa ce a jiya Alhamis.

A na sa ran zai yi takara tare da shugaban jam’iyyar na yanzu, John Odigie-Oyegun, idan har Oyegun din ya fito takara.

Dukkan su biyu sun fito daga jihar Edo ne.

Taron da shugabannin jam’iyyar na jihohi suka gudanar na yankin Kudu-maso-kudu, ya karke da sa-in-sa, dalilin bukatar bangarorin mutanen biyu masu neman shugabancin jam’iyyar.

Ana yada jita-jitar cewa Oshimhole na da goyon bayan Shugaba Muhammadu Buhari. Kuma ana yi masa kallon wanda ke samun goyon bayan jagoran APC, Bola Tinubu.

Share.

game da Author