‘Yan sanda sun tarwatsa cincirindon ‘yan Shi’a a Abuja

0

Rundunar ‘yan sandan Abuja ta tarwatsa dandazon mabiya Shi’a da ke zanga-zangar neman a saki jagoran su, Sheikh Ibrahim Zakzaky.

Wanda aka yi abin kan idon sa, ya bayyana cewa sun gudu ganin yadda jami’an tsaro ke harbin kan-mai-uwa-da-wabi na albarushin barkonon tsohuwa a daidai Dandalin Unity Faountain, inda nan ne matattarar masu zanga-zangar fiye da kwanaki 90.

Dama dai cikin makon da ya gabata sai da kami’an tsaro suka hana a yi zaman dirshan a wurin, kuma aka girge ‘yan sanda har a kan dawakai ana tsaron dandalin.

A wurin ne dai aka kama dan taratsin kwatar ‘yanci Deji Adeyanju a ranar 12 Ga Afrilu, kuma daga nan ne aka haramta yin taro a wurin ko da na lumana ne.

Sai dai kuma a wata takarda da kakakin kungiyar Ibrahim Musa ya saka wa hannu ya bayyana cewa suma sun far wa ‘yan sandan da suka nemi tarwatsa su.

A wani Bidiyo da ya karade shafunan yanar gizo wanda PREMIUM TIMES tayi kicibus da shi, an ga yadda babbar motar ‘Yan sanda ke ta yi wa ‘yan shi’a aman barkonun tsohuwa da ruwan zafi, su kuma suna ta jifar motar da duwatsu, sanduna, kwanuka, wasu kuma suna kokarin hawa motar domin ko za su iya tsayar da ita ko su fizgo direban motar.

Share.

game da Author