2019: INEC ta karyata ji-ta-ji-tar fara daukar ma’aikata

0

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta yi kira ga jama’a da su yi watsi da wani bayani da aka yada a soshiyal midiya cewa ta na daukar ma’aikatan da za su yi aikin zaben 2019.

INEC ta ce wannan labari ko kusa ba haka ba ne, kuma ba ta san daga inda wannan labari ya fito ba.

Hukumar Zaben ta ce ta na sane da cewa wasu kafafe a online sun bada sanarwar INEC za ta dauki ma’aikata na kayyadadden lokaci har guda dubu 100, domin su yi mata aikin gudanar da zabukan 2019.

Hukumar ta kuma roki mutane cewa su yi biris da duk wata sanarwa da aka ba su, har sai sun tabbatar daga inganci da sahihancin maganar daga INEC tukunna.

Share.

game da Author