Hankali na ya na kan tsaro da tattalin arziki, ba kan zaben 2019 ba -Buhari

0

A wata ganawa da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi da Firayi Ministar Birtaniya, Theresa May, shugaban ya bayyana cewa bai damu da takarar 2019 ba, domin hankalin sa na kan magance matsalar rashin tsaro da kuma tattalin arziki.

Buhari da May sun yi wannan tattaunawa ce a wata ganawa da suka yi, a Gidan Gwamnatin Birtaniya da ke lamba 10 kan Titin Downing, a Landan.

“Kafin mu hau mulki mun yi kamfen a kan muhimman abubuwa uku – samar da tsaro a kasa, farfado da tattalin arzki da kuma yaki da cin hanci da rashawa. To akwai zabe kuma na tafe cikin shekara mai zuwa, tuni har ‘yan siyasa sun maida hankulan su a kan zaben, amma dai ni ban damu ba, na fi damuwa game da tsaro da tattalin arziki.”

Buhari ya ci gaba da cewa Najeriya da Birtaniya sun dade da cimma hadin kai a tsakanin su ta fannoni da dama.
“Ya kamata mutane su san yadda suka kawo a matsayin da suke a yanzu idan har su na so su ci gaba. Amma sai aka tafka kuskure a baya-bayan nan har aka daina koyar da darasin tarihi a makarantun mu. Amma gwamnatinmu kuma a yanzu za mu maido shi a cikin manhajar darussan da ake koyawa a makarantu.”

Buhari ya kuma yaba wa wasu kamfanonin Birtaniya irin su Cadbury, Unilever da wasu da dama, wadanda ya ce, “sun jajirce a Najeriya duk rintsin wahalhalu da matsaloli, tun kafin Yakin Basasa, ta inda har a lokacin yakin Basasa ma ba su kwashe na-su-ya-na-su sun fice daga Najeriya ba.”

“Amma duk da haka mu na bukatar karin wasu masu zuba jarin daga nan Birtaniya domin su shigo Najeriya. Muna kuma godiya dangane da goyon bayan da ku ke bayarwa na kayan aiki da kuma bayar da horo ga jami’an sojojinmu, musamman a lokacin da muke yaki da Boko Haram. Amma mu na so mu ci gaba da hulda da ku a fannin kasuwanci da zuba jari.”

Buhari ya kuma bayyana wa Firayi Ministar kokarin ci gaban da aka samu a Najeriya a fannnin noma, inda ya furta cewa a yanzu mun rage shigo da shinkafa ya zuwa kashi 90 bi sa 100, ta yadda a yanzu Najeriya ce ke ciyar da kan ta daga cikin gida ba sai an dogara da shigo da abinci daga waje ba.

Ya kuma yi bayani dangane da wasu fannonin daban.

Share.

game da Author