Ofishin Hukumar Zabe na Jihar Kaduna ta babbake

0

Da safiyar Asabar din yau ne gobara ta tashi a hedikwatar Hukumar Zabe ta Jihar Kaduna inda wutar ta babbake ofishin dake titin Sokoto.

Duka-duka bai wuce makonni 3 zuwa 4 ba da za ayi zaben kananan hukumomi a Jihar.

Tun bayan yin zabukan fidda ‘yan takara na jam’iyyar APC da akayi a jihar akayi ta kai ruwa rana tsakanin jami’an gwamnati da ‘yan takara da suka yi ta zargin sun yi musu karfa-karfa wajen kakaba musu yan takarar da basu so ba.

Abin bai yi dadi ba matuka inda har zanga-zanga wasu ‘yan takara suka yi a Jihar.

Har yanzu dai ba a fadi sanadiyyar tashin wannan gobara ba, sai dai masu yin fashin baki sun ce da ‘walakin goro a miya.’

Share.

game da Author