PDP: Yunkurin Yi Wa Buhari Taron Dangi a 2019, Karin Haske Ko Karin Duhu?

0

Jam’iyyar PDP da ta shekara 16 ta na mulkin Najeriya, ta gamu da ajalin ta a kan mulki a zaben 2015, bayan da gamayyar jam’iyyun adawa suka yi mata taron dangi, duka yi mata kwaf-daya. PDP ta ji jiki sosai, domin baya ga kwace mata shugabancin kasa da aka yi, jam’iyyar adawa APC ta lashe jihohi 24, inda duk gwamnonin su na APC ne.

Wannan ya kawo karshen tinkaho da bugun kirjin da PDP ta rika yi cewa sai ta yi shekara 50 ta na mulki, sannan za a huta ta ba jam’iyyar adawa ita ma ta dandana, bayan zango daya kuma ta kwace abin ta.

Sai dai kuma wani abin dubawa, karfin jam’iyyun da suka game ba shi ne ya kayar da PDP kadai ba. Babban dalili shi ne rikicin cikin gida wanda ya tirnike jam’iyyar, har ya fusata wasu gwamnoni su ka yi wa jam’iyyar fitar burtu, su ka komawa APC.

Ta kasance a lokacin duk wadanda aka bata wa rai daga cikin PDP, sai su tuma tsalle su tinjima cikin rijiyar APC mai zurfi gaba dubu.

Daga cikin gwamnonin APC 24 da suka ci zaben 2019, guda 17 duk gyauron PDP ne. Haka nan akwai sanatoci da dama wadanda asalin su duk ‘yan PDP ne, amma suka shiga rigar APC aka kafa mulki da su.

Shi kan sa Shugaban Majalisar Dattawa Saraki, asalin sa Gwamnan PDP ne, kuma sanatan PDP ne, kafin ya balle ya koma APC. Ga kuma tsohon Kakakin Majalisar Tarayya, Aminu Tambuwal, shin ma dan PDP ne.

Kakakin Majalisar Tarayya, Yakubu Dogara, ya yi wakilci har zango biyu a baya a karkashin PDP.

Minsitan Gona Audu Ogbe da Sanata Barnabas Gemade da ke Majalaisar Dattawa a yanzu, kowanen su ya taba yin shugabancin jam’iyyar PDP, amma yanzu duk da rigar mutuncin APC suka shiga gwamnati, bayan da suka farke rigar mutuncin PDP suka jefar.

Shin wai ko dama can idan ka debe Buhari da gayyar Bola Tinubu, babu wata APC, abin duk ‘yan PDP ne?

Ko shakka babu kayen da PDP ta sha ya gigita ta, kuma har yanzu wasu ‘ya’yan na ta ba su daina fita daga cikin jam’iyyar ba.

Sai dai kuma wannan ba zai taba zama wani dalilin da zai sa a ce PDP ta gurgunce ba. Idan ma ta dan gurguncen, to masu kallon kokawa ai sun sha ganin inda gurgu ya yi wa mai kafafu lalata, ya tadiye shi da kafa daya ya fadi.

YUNKURIN YIN ‘MAJA’ DA PDP

A wani taron gaggawa da masu ruwa da tsakin PDP suka gudanar ranar Alhamis a Abuja, shugaban jam’iyyar Uche Secondus, ya bayyana cewa sun tattauna yiwuwar karkato hankulan sauran jam’iyyun siyasa domin a hada hannu wuri guda a kayar da APC a zaben 2019.

Daga nan kuma ya yi kira tun daga manya, kanana, matasa, jam’iyyu, kungiyoyin sa-kai da shugabanni duk a runtumo a yi maja domin a fyado gwamnatin APC daga kan kujerar mulki.

Share.

game da Author