Wasu mahara sun kashe mutane biyar a harin da suka kai kauyen indin dake karamar hukumar Barikin Ladi, jihar Filato.
Bayan haka wasu mutane 3 sun sami rauni a harin.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Terna Tyopev ya tabbatar wa PREMIUM TIMES wannan hari.
Yace an kai harin ne a daren Lahadi.
” Ba zan iya bada bayanai kan ainihin abin da ya faru ba yanzu, sai dai ina kira ga matasa su dai na yada jitajita.”
Discussion about this post