Gaskiya bana tare da masu zagin shugabanni kuma ban yarda a zira musu ido ba idan sun karkace.
Masu ilimi sun ce da shugaba da mace da yaro da kuma mahaukaci dole sai an dinga saitasu a hanya. Abun da muke cewa kullum shine, kowa ya yi hakuri da son zuciya don kowa yaji dadin Najeriya tsakanin talaka da mai mulki. Kasarmu tana da dadi wallahi idan an gyara ta.
Abunda zai baku tsoro shine sama da shekara Talatin ana sata a Najeriya amma gashi Allah ya rike mana arzikin kasar kuma mu talakawan muna nan yunwa bata kashemu ba. Kai kana tunanin da rayuwar talakawan Najeriya a hannun masu satar take zasu kai sama da miliyan dari yanzu? Ai ko ciwon zuciya zai iya kashe miliyan talatin daga cikinsu kafin azo maganar ciwon talauci wanda yafi cutar Ebola karfi.
Akwai takaici a cikin siyasar mu,a lokacin da ‘dan takara yake neman kuri’a har ruku’u yake yi a gaban dattijen garin ku don ya samu karbuwa amma daga zarar yaci zabe sai ya dinga sabani daku saboda dama yana so ya hau kujerar ne don ya kwaso rabon sa a dukiyar kasa. Dama an raba gadon jihar mu ko kasar mu ne da wani zai kwashi rabon sa? Haka rannan mun dawo daga tafiya, mun biyo ta Hadejia sai naga gayyar matasa suna ta daga adda sun cika titi da fastocin wani mutum. Can sai gashi nan a saman wata katuwar jeep duk an danneta da samari sai nayi dariya nace Allah yasa kwalliya ta biya kudin sabulu.
Amma muji tsoron Allah, don wannan kalmar ita kadai ce ake fadawa mazajen kwarai jikinsu yayi sanyi. Idan yau mune gobe bamu bane,yanzu ina wadanda suka yi mulki daga 1999 zuwa 2003 da 2007? A lokacin sune masu yin doka, sune masu zartarwa amma yanzu tun daga bishiyoyin gidajen su zaka gane suna jin jiki kuma gashi suna yawo da hakkunan talakawa akan su idan sun yi sata kenan. Kai kasan cewa akwai masu mulkin wancen lokacin da suke sana’a a kasan talakawa yanzu?
Allah ya shiryar damu.
Discussion about this post