KURUNKUS: Buhari zai sake tsayawa takarar shugabancin kasa a 2019

0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amsa kiran da yawa daga cikin masoyan sa da ke ta kiran sa da ya fito takarar shugabancin Najeriya a 2019, wato yayi tazarce.

Buhari ya yi wannan bayyana haka ne a wurin taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC da yake guna a Abuja.

A taron da yanzu haka ana can ana gudanar da ita a hedikwatar jam’iyyar APC a Abuja, an ce Buhari ya fadi haka ne bayan ‘yan jarida sun fice daga dakin taron.

Shugaban Masu rinjaye a majalisar tarayya, Hon. Ado Doguwa daga Kano, ya tabbarar wa PREMIUM TIMES cewa lallai Buhari zai sake tsayaya takara.

Bayan haka duk a wannan taro da yake gudana yanzu, jam’iyyar ta haramta wa shugabannin jam’iyyar da ke kan kujerun mulki na jam’iyyar sake tsaya wa takara sai dai idan jam’iyyar tayi musu lamini a shirin sake zaben shugabannin jam’iyyar da take yi.

Share.

game da Author