Kungiyar ma’aikatan Kiwon lafiya na Najeriya,JOHESU za su fara yajin aiki a fadin kasar nan.
JOHESU dai kungiya ce da ke da iko da duk wani ma’aikacin jinya wato Nurses, da masu aiki a fannin bada magani a asibitocin kasar nan.
Kamar yadda mataimakin Shugaban Kungiyar Ogbonna Chimela, ya bayyana, wa’adin da Kungiyar taba gwamnati ya cika cif a daren litinin din nan ne.
Ya ce muddun gwamnati bata ce komai akai ba toh zasu rufe asibitoci gaba daya sannan duk sauran mabiyan su a jihohi ma za su bi sahu.
Sai dai kuma Ministan Kiwon Lafiya Isaac Adewole ya ce gwamnati na ta fadi-tashi don ganin Kungiyar bata Kai ga far yajin aikin ba.