Wasu likitoci a makarantar gudanar da bincike na ‘Hygiene da Tropical Medicine’ da ke kasar Landan sun gudanar da bincike kan inganta gidajen sauro don kare mutane daga kamuwa da zazzabin cizon sauro.
Likitocin sun bayyana cewa a binciken su sun gano cewa zuba maganin ‘Piperonyl Butoxide’ da suka yi a gidajen sauro ya samar da kariya fiye da gidajen sauron da aka sakawa maganin ‘Pyrethroid’ inganci.
Bayan haka sun ce wasu daga cikin dalilan da ya sa suka yi wannan bincike shine don su samar da gidajen sauron da zai taimaka wajen ba wa mutane kariya daga cizon sauro da zazzabi.
Kungiyar kula da kiwon lafiya ta duniya (WHO) wacce ta goyi bayan wannan binciken ta bayyana cewa hakan zai taimaka wajen kare mutane daga kamuwa da cutar da dalike yaduwar ta.