Kungiyar EU ta tallafawa gidauniyar ‘Zabiya’ da Naira miliyan 70

0

Shugaban gidauniyar mutane ‘Zabiya’ Jake Epelle ya bayyana cewa kungiyar kasashen turai (EU) ta tallafa musu da Naira miliyan 70.

Epelle wanda ya sanar da haka ranar Litini wa kafanin dillancin labaran Najeriya a Abuja ya ce EU ta tallafa musu da wannan kudi ne domin gudanar da bincike kan yadda za a inganta rayuwar irin su a kasar nan.

Ya ce za su yi amfani da wadannan kudade kuma wajen sarrafa man shafawan dake kare au zabiyan daga cutar da Kan kama fatar su daga hasken rana, kaifafa kwarin idanuwar su da sauran su.

Epelle ya kuma kara da cewa sun hada guiwa da hukumar gudanar da kidaya ta kasa domin taimaka wa duk Zabiyan dake kasar nan.

” A yanzu haka gidauniyar mu na aiki a jihohi shida da Abuja a kasar nan sannan za mu bukaci Naira miliyan 400 zuwa 500 Idan har muna so mu kai ga ci.”

” Muna sa ran cewa bayan mun gudanar da wannan binciken za kuma mu sami karin kudade daga sauran kungiyoyi don bunkasa aiyukkan mu’’

A karshe Epelle yace duk da matsalolin da suke fama da su wajen gano da taimaka wa Zabiyan da suke kasar nan ba za suyi kasa-kasa na wajen ganin sun hado kan dukkan su.

Ya kuma ce za su zauna da hukumar kula da zabiya na kasa don ganin sun samar wa irin wadannan mutane ingantaciyyar kiwon lafiya kyauta a kasar.

Share.

game da Author