2019: Buhari ya nada Festus Keyamo daraktan yada labaran kamfen

0

Kwana daya bayan Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa batun zaben 2019 ba ya gaban sa, sai ga shi kuma ya ba da sanarwar nada fitaccen lauya Festus Keyamo a matsayin kakakin yada kamfen da tsare-tsaren shirin tazarcen sa.

Nadin da aka yi wa Keyamo na cikin wata wasika da Rotimi Amaechi ya sa wa hannu a ranar 16 ga Afrilu.

Amaechi shi ne Darakta-Janar na kamfen din Buhari kuma Ministan Sufuri.
Keyamo na daya daga cikin masu shiga gaban goyon bayan Buhari, tun bayan zaben 2015.

Share.

game da Author