Rahoto na musamman da PREMIUM TIMES Hausa ta buga a ranar Juma’a, ya tabbatar da Adeosun, Saraki, Dogara da Akanta Janar Ahmed Idris sun yi wa naira bilyan 10 rabon-tuwon-gayya, kuma an kawo muku yadda Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki da Ministar Harkokin Kudade, Kemi Adeosun suka yi wa PREMIUM TIMES borin-kunya.
Yau kuma ga mu dauke da jerin sunayen kamfanonin da a wancan lokacin muka bada rahoton cewa ba su da rajistar cancanta aka ba su kwangilolin, har su 44, amma kuma aka raba musu naira biliyan 5.638.
Raba musu kudaden a lokacin mulkin Buhari haram ne, domin Sakataren Gwamnatin Tarayya a lokacin mulkin Goodluck Jonathan, Anyim Pius Anyim, ya fitar da doka a ranar 11 Ga Disamba, 2014 cewa an hana bada kwangila ga duk wani kamfanin da ba shi da rajista da Hukumar Rajistar Kamfanonin Kwangilar Gwamnatin Tarayya. Dama kuma akwai wannan dokar da aka kafa, wadda aka yi wa gyara tun cikin 2007, ta na aiki daram.
Kamfanonin su ne:
Mushin Motors,
Assamad Procurement and Services Limited,
Kaffe International Investment Limited,
Quantita Services Nigeria Limited,
Dua Creations Limited,
Lachoso Engineering Systems Nigeria Limited,
Navadee Integrated Nigeria Limited,
Starcraft Integrated Limited,
Wadatu Global Company Limited,
Bimfirst Multiventures Limited,
Pimpex Engineering and Construction Company Limited,
Three Brothers Concept Nigeria Limited, Braimuh Nigeria Limited,
Unified Marketing Limited,
H and H Inter-Biz Services,
Nsa-Nsa Communication and O.B. Global Intertech Limited.
A.A. Marmaro Nigeria Limited,
Nwezei Merchandised Limited,
Jaaniyat Inter Concept Limited,
Kamawalay Global Nigeria Limited,
Popona Star Nigeria Limited,
Yujam Nigeria Limited,
D.C. Okika Nigeria,
Paki International Motors Limited,
Afric Capital Nigeria Limited,
Liberty Synergy and General enterprises,
Pranav Contracting Nigeria Limited,
Dee Ex Associate Limited,
Shazamzam Construction Limited,
Omatie Global,
Bilmos Nigeria Limited,
Clario View Nigeria Limited,
Esyad Nigeria Limited,
Omaiauto Limited,
Profile Project Nigeria Limited.
Chancellors Court Limited,
M/S Atlantic Authos Limited,
Bestline Nigeria Limited,
Geoafriqcom Sourcing and Services Limited,
DCN Nigeria Limited,
Emerging Giant, GSES Nigeria Limited,
Saramin International Ventures Limited.
Bayan haka, baya ga cewa wadannan kamfanoni ba su da rajistar cancanta karbar kwangila daga Hukumar Tattara Kamfanonin Da Suka Cancanta, 17 daga cikin su kwata-kwata ko rajistar takardar tsire daga Hukumar Rajistar Kamfanoni, CAC ba su da ita.
Alhali kuma tun a cikin 1990 aka kafa dokar haramta bada kwangila ga kamfanonin da ba su da rajista. Dokar kasa ta ce yin haka laifi ne, zamba ce kuma harkalla ce mai munin gaske.