ZAZZABIN LASSA: Akwai yiwuwar kasar Saudi za ta hana ‘yan Najeriya yin aiki Hajji bana

0

A sanadiyyar bullowar zazzabi lassa da aka tabbatar da yaduwar ta a jihohi 20 na Kasar nan, kasar Saudiyya na shirin taka wa Najeriya birki daga zuwa aikin hajjin bana.

Jihohin da aka samu rahoton bullowar cutar sun hada da, Anambra, Bauchi, Benue, Delta, Ebonyi, Edo, Ekite, Federal Capital Territory, Gombe, Imo, Kogi, Lagos, Nasarawa, Ondo, Osun, Plateau, Rivers, da Taraba.

Kamar yadda wani rahoton Kungiyar Kiwon Lafiya ta Duniya ya fitar, mutane 1081 ne suka kamu da cutar inda 90 daga ciki sun riga mu gidan gaskiya.

Bayan haka rahoton ya nuna cewa akwai mutane 317 da aka tabbatar suna dauke da cutar, wasu bakwai kuma ba’a tabbatar da haka ba a kan su sannan mutane 70 sun rasu.

Sai dai kuma an dan samu raguwar wadanda suka kamu da cutar da kuma yaduwar sa a wannan wata na Afrilu. Kasa da mutane 20 ne ke kamuwa da cutar a duk mako sannan a karshe makon da ya gabata, mutane biyar ne kawai aka samu sun kamu da cutar.

Kakakin Hukumar Alhazai ta Kasa , Mousa Ubandawaki, ya bayyana cewa gwamnati fa bata ga ta zama ba, domin kuwa a haka ma akwai zama ta musamman za ayi da hukumomin Saudi da jami’an gwamnati da ya hada da shugabannin hukumar na jihohi a wannan mako.

Za a to ganawar ne a ofishin Sakataren gwamnatin tarayya domin shawo kan matsala.

Share.

game da Author