Yadda Buhari ya kwashi dala miliyan 462 ba tare da sanin Majalisar Tarayya ba

0

Tabbatattun bayanai sun nuna cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba hannun amincewa a kwashi dala milyan 462 daga asusun gwamnatin tarayya, aka bai wa Gwamantin Amurka domin sayo jiragen yaki 12, ba tare da amincewar Majalisar Tarayya kamar yadda dokar kasa ta bayyana ba.

Shugaba Buhari dai ya yi rantsuwa da Alkur’ani cewa ya yi alkawarin zai yi aiki a kan yadda ka’idar tsarin mulkin Najeriya ya gindaya. Kuma irin wannan abin da ya yi ne ya ce ya zo ya gyara irin wanda gwamnatin baya ta rika yi.

Idan za a iya tunawa, Gwamna Ayo Fayose ya ce bai yarda a cire kudin ba, domin wayau ne gwamnatin Buhari za ta yi, don ta kwashi kudin kamfen na zaben 2019, shi ne ita ma ta cire kudi da sunan cinikin makamai.

Dokar Najeriya ta ce Shugaba ba shi da ikon sa hannu ya kwashi kudi ko bayar da iznin a kwasa daga Asusun Gwamnatin Tarayya, ba tare da amincewar Majalisa ba.

Sai dai kuma wata wasika da shugaba Buhari ya aika wa Majalisar Tarayya daga baya, ya fake da cewa Gwamnatin Amurka ce ta bayar da wa’adin wasu kwanaki, cewa kada Najeriya ta wuce kwanakin ba tare da ta bayar da kudin ba. Wannan shi ne dalilin da ya sa Buhari ya yi riga-malam-masallaci ya sa a hannu a cire kudaden Majalisa ba ta sani ba.

Buhari ya aika da wasikar ranar 13 Ga Afrilu, amma sai ranar 17 Ga Afrilu wasikar ta je ofishin Kakakin Majalaiar Tarayya.

Sai dai kuma wasikar ta nuna cewa sanarwa ce kawai aka yi, domin an rattaba cewa an rigaya an sa hannun cire kudaden, da kuma dalilan da suka sa aka yi gaggawar cire su ba da izni ba.

A cikin wasikar da Buhari ya aika wa Majaisar Tarayya, ya shaida wa Saraki da Dogara cewa tunda dai dama kowa na sane da wannan batu tun bayan wani taro da ya yi da gwamnoni, cikin watan Disamba, inda suka nuna amincewa a cire kudin, to tuni an ma cire kudin an kuma tura a cikin asusun gwamnatin kasar Amurka

Buhari a ce za a sayo jiragen yaki ne guda 12, saboda matsalar tsaro. Adadin kudaden inji Buhari sun kai dala miliyan 496,374,470.00, watau kwatankwacin naira biliyan N151,394,421,335.00 cif da cif.

Daga nan sai ya roki majalisa da cewa, tunda dai ya rigaya ya cire kudin ba tare da amincewar su ba, ya na rokon su rubuta adadin kudaden a cikin kasafin kudi na 2018 kawai, maganar ta wuce.

Daga nan sai ya ce sauran kudin kuma da ba a rigaya aka cire ba, tunda dama dala biliyan daya ce za a cira, to nan gaba idan sauran hukumomin tsaro sun gama gabatar da abubuwan da suke bukata, sai shi Shugaban kasa ya gabatar wa majalisa da bukatun, ba zai yi azarbabin cirar kudi nan gaba ba tare da ya tsallake majalisa ba.

Idan ba a manta ba, farkon watan nan ne Ministan Tsaro Mansir Dan’Ali ya bayyana wa manema labarai a fadar Shugaban Kasa cewa Buhari ya sa hannun cire makudan kudaden.

Wannan magana ta tashi hankulan jama’a da dama a kasar nan, inda nan da nan Majalisar Tarayya ta ce ita dai Buhari bai sanar da ita ba, kuma bai nemi iznin ta ba.

Nan da nan hadiman Buhari suka fara bayanin cewa ai ba zai cire kudin ba tare da ya sanar da majalisa ba.

Amma abin mamaki, sai ga shi bayanai sun nuna cewa an ma cire kudin, kuma sai bayan da aka cire ne sannan Buhari ya aika wa majalisa takardar sanar da cire kudin, amma ya roke su da cewa a tari gaba.

Share.

game da Author