Wani kwararren likita mai suna Oyewale Tomori ya koka kan yadda Najeriya taki maida hankali wajen kawar da cutar zazzabin Lassa da yake neman ya addabi mutanen kasar.
Tomori ya yi wannan furuci ne da yake tofa albarkacin bakin sa a taron wasu kwararru da akayi kan yadda za a samar da hanyoyin dakile yaduwar cutar da kuma samo maganin ta.
A bayanan sa ya rika yin misali da yadda cutar ta yadu a kasar nan in da mutane 394 suka kamu da cutar sannan 95 suka rasu a dalilin kamuwa da cutar.
Ya ce cutar zazzabin Lassa wanda aka gano ta shekaru 49 da suka wuce a wata kauye a jihar Barno ta ci gaba da yi wa rayukan mutanen kasar nan barazana sannan har yanzu ba a iya gano yadda za a magance matsalar gaba daya ba.
Yayi tsokaci da rashin kudi da asibitoci na musamman da wadanda suka kamu da cutar za su samu kula ta musamman, da kuma irin loda wa sanatoci da ‘yan majlisa kudade maimakon a karkata su wajen inganta fannin kiwon lafiya.
Bayan haka jami’ar hukumar NCDC Elsie Ilori ta ce tabas yadda cutar zazzabin Lassa ta yadu a Najeriya a wannan shekarar ya yi matukar tada musu da hankali ganin irin shirin da gwamnatin tarayya tayi na hana yaduwar cutar a kasar.
” Gwamnatocin jihohi ne suke bamu matsala a ayyukan mu domin ba ma samun isassun bayanai kan yaduwar cututtuka da matsayin kiwon lafiyar mutanen jihohin su. Haka na matukar dama mana lissafi a ayyukan. Kusan dukkan su sun zauna ne dirshen suna jiran gwamnatin tarayya tayi musu komai maimakon suma suyi hubbasa a jihohin su.