An kaddamar da dalar shinkafa ta farko a Maiduguri

0

Gwamnan jihar Barno, Kashim Shettima ya kaddamar da dalar shinkafa ta farko a filin wasa na Ramat dake Maiduguri.

Manoman da suka amfana da shirin samar wa manoma bashi na gwamnatin tarayya (Anchor Borrowers Programme) ne suka noma shinkafar a fadin jihar.

Manoman su 18,000 sun hallara filin wasa na Ramat inda aka jera wadannan buhuna na shinkafa a bainar jama’a.

Kananan hukumomin da ba su yi fama da ta’addancin Boko Haram ba ne suka amfana da wannan shiri sannan an tabbatar wa manoman cewa ‘yan kasuwa a shirye suke da su siye shinkafar.

Kananan hukumomin sun hada da Jere, Konduga, Mafa, Biu, Hawul da Shani.

Share.

game da Author