WHO ta ware dala miliyan 178 domin kawar da cututtuka a Najeriya

0

Wani Jami’in kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) Wondimagegnehu Alemu ya bayyana cewa kungiyar WHO ta ware dala miliyan 178 domin tallafawa Najeriya wajen kawar da wasu cututtuka har na tsawon shekaru biyu.

Alemu ya sanar da haka ne ranar Litini yayin da yake tattaunawa da ministan kiwon lafiya Isaac Adewole a Abuja.

A bayanan da ya yi Alemu ya ce za a kashe dala miliyan 127 wurin kawar da cutar shan inna, Za kuma a kashe dala miliyan 30 wajen kawar da cututtukan da aka fi kamuwa da su a kasar kamar su zazzabin cizon sauro, tarin fuka da cutar Kanjamau.

Ya kuma kara da cewa dala miliyan 8.1 kuwa za a kashe su wajen inganta kiwon lafiyar mata da yara kanana sannan da dabarun bada tazarar haihuwa sannan sauran kudaden za a yi amfani da su ne wajen hana bullowar cututtuka a kasar.

Share.

game da Author