ASARI BAI FADI GASKIYA BA: Makarfi bai zabi APC ba a 2015

0

Kakakin tsohon gwaman Jihar Kaduna, kuma tsohon shugaban Jam’iyya PDP, Sanata Ahmed Makarfi, Mukhtar Siraj ya karyata hirar da akayi da Dan taratsin nan na yankin Neja Delta, Asari Dokubo in ya fadi cewa wai Makarfi ya zabi jam’iyyar APC a zaben shugaban Kasa, sannan kuma bai tsaya a zaben ba sai da ya nuna wa jama’a takarda da ya dangwala zaben kuru-kuru su shaida.

Siraj ya karyata wannan korafi na Asari cewa yabo zance kawai yayi babu kanshin gaskiya dake tattare da hakan.

A wata doguwar takarda da ya saka wa hannu, Siraj ya kara da cewa Makarfi mutum ne mai dattaku sannan mai ra’ayi da duk da matsalolin da jam’iyyar PDP ta yi fama da su, bai taba nuna gazawar sa wajen ci gaba da ya yi wa jam’iyyar hidima ba.

” Makarfi na da damar ya canza sheka amma bai yi haka ba, ya tsaya duk rintsi domin ganin jam’iyyar ta farfado daga matsalolin da ta Sami kanta a wancan lokacin.

” Sanin kowa cewa Makarfi ba zai yi wannan abu Asari ya fadi ba amma mutane da ke wannan wurin zabe shaida ne.

” Makarfi ba zai butulci jam’iyyar da ya bauta wa ba sannan a cikin ta ya rayu a siyasan ce. Yayi gwamna shekara takwas, yayi sanata shekara takwas sannan ya jagoranci jam’iyyar a lokacin da take cikin mawuyacin hali.

Siraj ya yi kira ga mutane da suyi watsi da wannan batu na Dokubo.

Share.

game da Author