An kama matasa biyu dake zambatar mutane da yi musu barazanar sace su a Jami’ar ABU

0

Shugaban jami’an tsaron jami’ar Ahmadu Bello dake Samaru Zariya jihar Kaduna, Jibril Tukur, ya bayyana cewa sun kama wasu samari biyu da ake zargin su da sace mutane a makarantar da unguwanin da ke makwabtaka da jami’ar.

Tukur ya sanar da haka ne da yake zantawa da kamfanin dillancin labaran Najeriya a ofishin sa dake jami’ar a Samaru.

Ya ce sun kama Halliru Sani mai shekaru 25 da Abdullahi Musa dan shekara 30 bayan sun saurari barazanar kisan da suka yi wa wani babban malamin jami’ar mai suna Keku Philip.

‘‘Philip ya fada mana cewa a ranar 26 ga watan Fabrairun wata lamba ta kira shi inda aka yi masa barazanar kisa idan har bai aiko da katin waya ba da ya kai na Naira 40,000.”

” Ya ce nan da nan sai ya rugo zuwa ofishin mu ya bayyana mana abin da ke faruwa sannan mu kuma muka shiga farautar su.

Bayan bincike da suka yi sai suka gano cewa ashe-ashe daya daga cikin masu garkuwan, Halliru dan uwan Philip ne, ya hada baki da abokin sa Abdullahi domin su cuci Philip.

Tukur ya jinjina wa jami’an tsaron makarantar , kuma ya ce za su ci gaba da samar da tsaro kamar yadda ya kamata.

Share.

game da Author