Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara Mohammed Shehu ya sanar cewa wasu ‘yan bindiga sun kashe mutane uku a kauyen Bawan Daji dake karamar hukumar Anka a jihar.
Shehu ya sanar da haka ne ranar Laraba inda ya kara da cewa maharan sun kai hari kauyen ne da safiyar Laraba.
Ya ce a daidai maharan na aikata wannan mummunar abu ne wasu mazaunan kauyen suka kira jami’an tsaro.
” Mun kora su a arangamar da muka yi sannan da yawan su sun tsere da raunin harsashin bindigogin mu.”
A karshe Shehu ya yaba wa mazauna wannan kauyen sannan ya ce su gaggauta sanar wa jami’an tsaro duk wanda suka ji an kai shi asibiti dauke da raunin bindiga.