Buhari ya jijjiga taron APC, ya soke karin wa’adi da akayi wa Oyegun, ya ce a dawo a yi zabe

0

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya umurci jiga-jigan jam’iyyar APC da ke ganawa a hedikwatar jam’iyyar a Abuja cewa a koma abi yadda dokar jam’iyyar ta gindaya na a yi zabe ne ba Kara wa’adi ga shugabannin jam’iyyar kamar yadda tayi a taron ta na watan Faburairu ba.

Buhari ya ce ya canza shawara ne bayan ganin cewa biye wa hakan zai iya jefa jam’iyyar cikin halin kakanikayi da shiga kuto.

Dama can da yawa daga cikin ‘yayan jam’iyyar na su amince da kara wa shugaban jam’iyyar Oyegun John da na jihohi wa’adin shekara daya da akayi ba.

Hakan ya sa wasu na ganin jam’iyyar APC ta dauki hanyar rugujewa daukar wannan shawara da ta yi.

Share.

game da Author