Lauratu Abdullahi, matar Tanko Yahaya ta shaida wa kotu a Kaduna cewa, a raba auren ta da mijin ta Tanko, saboda nisantar ta da yake yi wajen kwana.
Lauratu dai ta haihu da Tanko har sau biyar, sannan yanzu haka ma tana da cikin na shida amma babbar abin da ya fi dada ta da kasa shine har yanzu malam Tanko baya isar ta a gado sannan kuma baya iya wadata da abinci yadda ya kamata.
Da yake mai da zance, mijin na ta Malam Tanko ya ce wannan korafi da mai dakin sa Laure take yi ba haka bane domin kuwa yana iya kokarin sa, hasali ma a dalilin kokarin ne har gashi tana da cikin da na shida.
Kotu ta umurce su da su mai da su koma su tattauna a tsakanin su sannan su bayyana ranar 3 ga watan gobe tared da waliyyan su domin karkare maganar.
Discussion about this post