Tinubu, Saraki, Dogara sun kaurace wa taron jiga-jigan APC

0

Babban jigon jam’iyyar APC, Bola Tinubu, Shugaban majalisar Dattawa Bukola Saraki da Kakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara sun kaurace wa taron jam’iyyar, wanda ke gudana a hedikwatar jam’iyyar dake Abuja.

Idan ba a manta ba Tinubu bai halarci taron da akayi ranar litinin a fadar Shugaban kasa ba.

A taron na yau Talata ba shi kadai ba har da Shugaban majalisar Dattawa Bukola Saraki da Kakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara, duk basu halarci taron ba.

Buhari a taron na yau ya soke wa’adin shekara daya da jam’iyyar kara wa shugabannin jam’iyyar na kasa da jihohi.

Dama dai lokacin wa’adin na su ya ciki, amma sai aka kara musu wa’adin shekara daya a taron da uwar jam’iyyar ta gudanar cikin Fabrairu na watan jiya, a nar 28, aka kara musu shekara daya.

Wancan kari da aka yi musu, ya nuna cewa shugabannin na APC ba za su sauka ba, har sai an gudanar da zaben 2019 tukunna.

To dama kuma wannan kari da aka yi musu na shekara daya, bai yi wa babban jigon jam’iyyar, Bola Tinubu dadi ba, musamman domin shi da shugaban jam’iyyar, Oyegun ba su shan ruwa a cikin kofi daya.

A yau din nan kawai sai Buhari ya ba su mamaki, yayin da ya bayyana wa dimbin manyan ‘yan jam’iyyar da ke halartar taron cewa kowa ya shirya soke karin wa’adin da aka yi wa shugabanni a watan da ya gabata, “ domin ya kauce wa dokar jam’iyya da kuma dokar Najeriya.”

Share.

game da Author