Shugaban asibitin fadar shugaban kasa dake Aso Rock, Abuja (SHMC) Jalal Arabi ya bayyana cewa akalla mutane 710 ne akayi wa gwajin cutar koda kyauta a asibitin.
Ya fadi haka ne da yake zanta wa da manema labarai ranar a Alhamis a Abuja, sannan ya kara da cewa sun yi haka ne don ranar cutar Koda ta duniya.
” Mutane 200 ne muka yi niyyar yi wa gwajin amma kafin mu ankara sai da mu kayi wa mutane 710. Sannan kuma muna kira ga mutane da su rika mafani da wannan dama domin sanin matsayin su game da cutar.