Mazaunan kauyen Bangai dake karamar hukumar Riyom jihar Filato sun koka kan rashin asibiti da suke fama da shi a kauyen shekaru biyar kenan sai dai su nemi wata hanyar.
Mazauna kauyen Bangai mai gidaje akalla 1,500 sun bayyana cewa tun da rikici ya hada su da makiyaya a kauyen a 2012 aka rufe cibiyar kiwon lafiyar da suke da ita. Har yanzu ba a bude ta ba.
Dakacin kauyen Yakubu Bwede ya ce tun da ake rufe asibitin yayi ta rubuta wasika zuwa ga gwamnati don a bude asibitin amma har yanzu ba a ce musu komai ba.
Bayan haka wani malamin makarantar firamare dake zama a kauyen Bangai Dalyop ya fadi cewa a dalilin rashin asibiti a kauyen ana rasa rayukan mutane da dama.
” Yanzu a kauyen nan idan wanin mu ya kamu da rashin lafiya sai dai mu tafi gidan wacce take riki da makullen asibitin ta bamu magani sannan idan cutar ya fi karfin ta sai mu kama hanyar zuwa asibitin dake kananan hukumomin Makiria ko kuma Riyom.
Discussion about this post