Dalilan da ya sa muke boye kudaden mu daga sanin mazajen mu – Mata Aure

0

PREMIUM TIMES ta binciko ra’ayoyin matan dake zama a babban birnin tarayya Abuja kan wasu dalilan da ya sa suke boye kudaden su ko kuma suke yin asusu ba tare da mazajen su sun sani ba.

Bisa ga ra’ayoyin da muka jiyo daga bakin wasu matan aure sun nuna cewa mata kan yi haka ne idan akwai rashin yadda a tsakanin masoya ko ma’aurata, tsoran rabuwa (ko na aure ko mutuwa) da dai sauran su.

Wata ma’aikaciyar kiwon lafiya mai suna Jummai Danladi ta ce tana boye kudi daga sanin mijinta ne saboda babu sauran yadda a tsakanin su, komai zai iya faruwa.

Ita kuma Bunmi Ade ta ce boye kudi daga mijin ta shine ya fi mata sauki domin mijin na ta na da barnan kudi sosai

” Hakan ya sa nake boye kudi sannan duk lokacin da yake bukatan kudi sai na yi masa karya in ce arowa na yi a wurin aikin domin ya ririta kudin.”

Su kuwa Gift Emmanuel da Loveth Chukwuma sun bayyana cewa mazajen su basa taimaka wa ‘yan uwan su idan suna bukatar taimako, shine yasa suke boye kudaden su domin dudun irin wannan rana.

Bayan haka wata mai bada shawara kan zamantakewar aure Patience David ta bayyana cewa mata kan boye kudade daga mazajen su ne saboda rashin yadda, soyyaya da rashin garmamata da wasu mazan ba sa yi.

‘‘Idan har dai akwai irin wannan matsala a zamantakewar masoya dole ne a sami irin wadannan abubuwa na rashin yarda a tsakanin su.”

Share.

game da Author