Abubuwa 8 da za suyi tasiri a zaben 2019

0

Zaben 2019 zai zo da sabon salo, wai kiran Sallah da usur. A kan haka ne PREMIUM TIMES ta farka ruwan cikin shekarar ta yi duban yadda zaben zai kasance, domin tun yanzu kowa ya san matsayin sa. Kamar dai yadda Waziri Aku ya fara gasar bada labari mai taken:

“yaro tsaya matsayin ka, kada zancen ‘yan duniya ya rude ka.”

1. Kai-da-halin-ka: Talakawa ba za su yi “Sak” ba. Mafi yawa na da-na-sanin zaben wakilan su na jihohi, na tarayya da sanatoci har da wasu gwamnoni. Dalili kenan suke cewa a 2019 sai sun darje, duk inda nagari ya ke to can suke. Shi ya sa a yanzu ake yawan cewa “sun ci taliyar karshe.”

2. Buhariyya: Guguwar Buhariyya ba za ta yi tasiri sosai ba a 2019. Duk da cewa har yanzu akwai wadanda ba su ganin kuskure, talasuranci da laifukan Buhari da na gwamnatin sa ba, da yawa wadanda suka sha wahala kuma suka sadaukar da dukiyoyin su don Buhari, sun dawo su na cewa an sha su sau hudu daga 2003 zuwa 2015, kuma sun warke.

Kaifi da tasirin Buhariyya ya ragu sosai a Arewa saboda bazatan da gwamnatin APC ta yi na kasa kawar da wasu matsaloli sai ma wasu da ta kara haifarwa.

3. A-kasa-a-tsare-a-raka: Wadannan dama kalamai ne na ‘yan adawa. Gwamnatin APC ba za ta yarda ta yi wannan kasassabar ba, saboda kalamai ne masu haddasa jama’a su yi wa hukuma tunzuri. Ko an ce a yi din, to da wahala a sake saida rai a nemo suna irin 2015, an saida ran amma ba a samu sunan ba.

4. Lale-kati: A 2019 ko an fito da kati a saya don a tallafa wa Buhari, ba za a saya ba. Saboda wasu na ganin cewa sun saya amma ba su ganin riba a 2015 ba.

Ita kan ta APC yanzu ta kudance domin ta fitar da kasafin naira bilyan 14 da za ta ragargaje cikin 2018, domin shirya wa zaben 2019.

5. Mawakan siyasa: Mawakan APC ba za su yi tasiri a 2019 ba. Ko da mawashin aska za su wasa wasu gwamnonin ko APC kan ta, ba zabar su za a yi ba.

6. Kwankwasiyya: Guguwar Kwankwasiyya za ta yi tasiri a zaben 2019. Duk inda Kwankwaso ya koma, mabiyan sa za su bi shi – “ko jam’iyya ce mai daudawa da kuka” kamar yadda mawakin sa Aminu Dumbulum ke cewa. Ko a kudancin kasar nan ana rade-raden cewa akwai alamomin yin ‘Red Cap Revolution’, wato Kwankwasiyya kenan.

7. Anti-party: Tabbas duk inda aka tsaida dan takarar da talakawa ba su so, to za a zabi dan wata jam’iyya daban.

8. Farfadowar PDP: Matsawar PDP ta tsaida wanda jama’a ke so, to za ta yi buga in buga da APC a Arewa. Za ta kwance wa APC zani a kasuwar Arewa ta Tsakiya. Za ta sake kwashe kuri’un Kudu-maso-kudu sannan za su yi canjaras a jihohin Yarbawa. Nasara kuma sai INEC ta kammala kidayar kuri’u.

Share.

game da Author