Akwai yiwuwar gano hanyar inganta kwayayen halitta a jikin mata – likita

0

Wata likita mai suna Coleen Murphy dake kasar Amurka ta gudanar da bincike inda ta gano hanyar kara inganta kwayayen halitta a jikin mata.

Murphy ta bayyana cewa ta gano haka ne bayan ta zuba wa kwayayen wasu tsutsosi da ba su riga sun hadu ba sinadarin ‘Cathepsin B.

Sakamakon da ta samu bayan yin haka ya nuna cewa sinadarin ya kara inganta yawan shekarun da kwayayen za su iya haihuwa ko da shekarun haihuwa na tsutsar sun wuce.

Murpy ta ce duk da cewa bata gwada sakamakon binciken a jikin ‘Dan Adam ba, ta ce nasarar da ta samu a wannan gwaji zai taimaka wajen kawar da wasu masalolin haihuwa kamar barin ciki da wasu matan kan yi fama da su saboda yawan shekarun su a lokacin da ta kammala aiki a kai.

Bincike ya nuna cewa matan da kan yi fama da barin ciki ba saboda rashin kwayayen halitta bane, an gano cewa rashin ingancin kwayayen halittar dake jikin su ba shi da lafiyar da zai iya rikida ya zama da saboda yawan shekaru.

Share.

game da Author